Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Taliban da wakilan Afghanistan na halartar tattaunawar sulhu a Rasha

Wakilan shugabancin Taliban da wakilcin gwamnatin Afghanistan na halartar tattaunawar zaman lafiya karkashin jagorancin Rasha can a birnin Moscow wadda ke da nufin kawo karshen yakinsu da gwamnatin kasar da aka shafe shekaru ana yi. 

Wannan ne dai karon farko da Taliban ke amincewa da makamanciyar tattaunawar wadda ake fatan ta kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru ana yi a kasar.
Wannan ne dai karon farko da Taliban ke amincewa da makamanciyar tattaunawar wadda ake fatan ta kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru ana yi a kasar. Reuters/路透社
Talla

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce halartar wakilcin bangarorinj biyu babban ci gaba ne ga yunkurin Rasha na ganin ta zama silar samuwar zaman lafiya a kasar ta Afghanistan da ta shafe shekaru ta na fuskantar tashe-tashen hankula.

Wannan dai ne karon farko da Taliban ke shiga makamanciyar tattaunawar da gwamnatin Afghanistan inda ta aike da wakilai 5 sai dai kakakin kungiyar Zabiullah Mujahid ya ce wakilcinsu ba zai kulla wata yarjejeniya da gwamnatin Afghanistan face samar da hanyoyin da za a ciyar da kasar gaba.

Taron wanda ya gudana a wani Otel da ke birnin Moscow na Rashan, yayin bude shi Lavrov ya ce fatansu shi ne ganin an samar da wata matsaya da za ta kawo karshen rikicin kasar, wanda shi ne mafarkin al'ummar Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.