Isa ga babban shafi
Amurka-Yemen

Amurka ta bai wa wata 'yar Yemen damar ziyartar danta mara lafiya

Kasar Amurka ta cire takunkumin bai wa mutanen da suka fito daga kasar Yemen biza ga wata mata, domin ziyarar dan ta wanda ke fama da rashin lafiyar da ake ganin ba zai tashi ba.

Matakin na Amurka ya biyo bayan zanga-zangar da aka rika gudanarwa a sassan birnin California don bayar da dama ga matar wadda ke neman ganin dan na ta da ke gab da mutuwa.
Matakin na Amurka ya biyo bayan zanga-zangar da aka rika gudanarwa a sassan birnin California don bayar da dama ga matar wadda ke neman ganin dan na ta da ke gab da mutuwa. Mercury
Talla

Wannan ya biyo zanga zangar da jama’a suka yi a wani asibiti da ke California, domin ganin shugaba Donald Trump ya ba da izinin bai wa Shaima Swileh, mahaifiyar Abdullahi Hassan, mai shekaru biyu, wanda dan kasar Amurka ne, damar ziyarar sa kafin ya mutu.

Bayan nuna mahaifin yaron cikin hawaye tare da masu zanga zanga, ofishin Jakadancin Amurka da ke Alkahira ya bai wa Shaima biza, yayin da kungiyar kare hakkin Musulmai ta ce tana kokarin ganin sun sa ta a jirgi domin isa kasar ta Amurka.

Dan na ta Abdullahi na fama da wani irin ciwon kwakwalwa ne da ba’a saba gani ba, kuma yanzu haka ya na amfani da inji ne wajen numfashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.