Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta haramtawa ‘Yan Turkiya Biza

Gwamnatin Moscow ta fara daukar mataki akan gwamnatin Ankara a yayin da suke ci gaba da cacar–baka tsakaninsu kan jirgin Rasha da Turkiya ta harbo a Syria a ranar Talata.

Vladmir Putin Shugaban kasar Rasha
Vladmir Putin Shugaban kasar Rasha Reuters
Talla

Rasha ta sanar da matakin dakatar da ba ‘Yan Turkiya izinin shiga kasarta, bayan ta yi gargadin daukar mataki mai tsauri akan Turkiya.

Ana sa ran dai shugaban Rasha Vladimir Putin zai hadu da Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan a taron sauyin yanayi da za soma a birnin Paris a ranar Litinin.

A ranar Talata ne Turkiya ta kakkabo jirgin yakin Rasha akan iyakar Syria, a wani mataki da ake ganin zai kara haifar da tankiya tsakanin kasashen biyu da ke da sabanin ra’ayi a rikicin kasar Syria.

Turkiya tace ta harbor Jirgin ne saboda ya sabawa dokokin sararin samaniyarta, yayin da Rasha ke cewa jirginta iyakar shi Syria bai tsallaka Turkiya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.