Mu Zagaya Duniya
Shugabannin kasashe na taron bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na 1
Wallafawa ranar:
Kunna - 20:02
Shirin Mu Zagaya Duniya ya yi waiwaye wanda masu iya magana suke cewa adon tafiya, kan wasu daga cikin muhimman al'amuran da suka faru cikin makon da ya kare, a sassan duniya. Daga cikin wadannan muhimman al'amura akwai taron da shugabannin kasashen duniya ke halarta na bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya a birnin Paris, wanda gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta joranci shiryawa.