Isa ga babban shafi
Syria

'Yan tawayen Syria sun dau matakin hana Soji shiga yankinsu

‘Yan tawayen Syria sun karya wasu manyan gadoji biyu da su ka hade yankin da ke karkashin ikon gwamnatin Bashar al Assad da yankin Idlib da ke karkashin ikon ‘yan tawayen kasar.Karya gadojin na daga cikin yunkurin ‘yan tawayen wajen ganin dakarun gwamnatin Syria ba su isa yankin tare da kwace iko da shi ba.

Yankin na Idlib dai shi ne yanki daya tilo da Syrian ke fatan fattatakar ‘yan tawayen cikinsa don kawo karshen rikicin kasar na kusan shekaru 7 da ya lakume rayuka fiye da dubu dari 3 da 50.
Yankin na Idlib dai shi ne yanki daya tilo da Syrian ke fatan fattatakar ‘yan tawayen cikinsa don kawo karshen rikicin kasar na kusan shekaru 7 da ya lakume rayuka fiye da dubu dari 3 da 50. ©REUTERS/Khalil Ashawi
Talla

Matakin karya gadojin biyu na zuwa ne bayan girke wasu tarin motoci da tankokin yaki wadanda ‘yan tawayen ke ganin yunkuri ne na fara yakarsu, yayinda a bangare guda ministan harkokin wajen Syriar Walid Mu'allem ya sha alwashin ganin bayan mayakan Alnusra ko da kuwa wacce irin sadaukarwa za su yi.

Gadojin biyu dai su ne suka hade yankin Hama da gwamnati ke iko da shi da kuma yankin Idlib da ya rage a hannun ‘yan tawayen kasar da suka kunshi mayakn Al-nusra reshen kungiyar Alqaeda da kuma Mayakan Hayat Tahrir al-sham.

Manufar karya gadojin a cewar kungiyar kare hakkin dan adam da ke sanya idanu kan rikicin na Syria shi ne ganin dakarun Syria ba su samu damar tsallakawa yankin ba, musamman bayan girke motocinsu na yaki da kuma yadda su ke shawagi a yankin na Idlib musamman garin Al-Ghab wanda da shi suka dogara wajen noma.

Yankin na Idlib dai shi ne yanki daya tilo da Syrian ke fatan fattatakar ‘yan tawayen cikinsa don kawo karshen rikicin kasar na kusan shekaru 7 da ya lakume rayuka fiye da dubu dari 3 da 50.

Kazalika matakin na zuwa a dai dai lokacin manyan kawayen Syriar da suka kunshi Rasha Turkiyya da kuma Iran ke shirin wani taro na musamman cikin watan Satumba don tattauna yadda za a kawo karshen yakin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.