Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Rashin kudi na barazana ga yaki da sauyin yanayi a duniya

Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bayyana cewar rashin isassun kudaden taimaka wa kasashe mataulata domin rage radadin sauyin yanayi na yi wa yaki da sauyin yanayin a duniya barazana.

Hayaki mai gurbata muhalli na daya daga cikin abubuwan da ke haddasa sauyin yanayi a duniya
Hayaki mai gurbata muhalli na daya daga cikin abubuwan da ke haddasa sauyin yanayi a duniya Reuters/Charles Platiau
Talla

An kafa asusun tallafa wa kasashe mataulata da ke fuskantar matsalar da sauyin yanayi ke haifarwa  a shekarar 2010 a wani zaman taron Majalisar Dinkin Duniya domin samar da Dala biliyan 100 kowacce shekara daga hannun kasashe masu hannu da shuni.

Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bayyana cewar ficewar kasar Amurka daga cikin yarjejeniyar Paris da kuma janye alkawarin bada kudaden da kasar ta yi za su jefa shakku wajen alkawuran da kasashen duniya suka dauka.

Ban ya ce, janye Amurka da shugaba Donald Trump ya yi zai haifar da tarnaki wajen tara Dala biliyan 100 nan da shekarar 2020 domin taimaka wa wadannan kasashe.

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi alkawarin sanya Dala biliyan 3 cikin asusun, amma ya zuwa yanzu Dala biliyan daya kacal aka bayar.

Daga cikin Dala biliyan 10 da aka yi alkawari a shekarar 2015, ya zuwa yanzu Dala biliyan 3 da rabi kawai aka samu domin gudanar da aikace -aikace a kasashe 78 na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.