Isa ga babban shafi
Ban Ki Moon

Karancin kudi na barazana ga shirin yaki da sauyin yanayi

Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bayyana cewar rashin isassun kudaden da za’a taimakawa kasashe mataulata domin rage radadin sauyin yanayi na yi wa yaki da sauyin yanayin a duniya barazana.

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya yi alkawarin sanya Dala biliyan 3 cikin asusun, amma ya zuwa yanzu Dala biliyan daya kacal aka bayar.
Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya yi alkawarin sanya Dala biliyan 3 cikin asusun, amma ya zuwa yanzu Dala biliyan daya kacal aka bayar. Reuters/路透社
Talla

An kafa asusun tallafawa kasashe mataulata da ke fuskantar kudar da sauyin yanayi ke haifarwa ne wajen taron Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2010, domin samar da Dala biliyan 100 kowacce shekara daga hannun kasashe masu hannu da shuni.

Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bayyana cewar ficewar kasar Amurka daga cikin yarjejeniyar Paris da kuma janye alkawarin bada kudaden da kasar ta yi zai jefa shakku wajen alkawuran da kasashen duniya suka dauka.

Mr Ban ya ce janye Amurka da shugaba Donald Trump ya yi zai haifar da tarnaki wajen tara Dala biliyan 100 nan da shekarar 2020 domin taimakawa wadannan kasashe.

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya yi alkawarin sanya Dala biliyan 3 cikin asusun, amma ya zuwa yanzu Dala biliyan daya kacal aka bayar.

Daga cikin Dala biliyan 10 da akayi alkawari a shekarar 2015, ya zuwa yanzu Dala biliyan 3 da rabi kawai aka samu domin gudanar da aikace aikace a kasashe 78 na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.