EU ta ci Google tara mafi tsanani a tarihi
Kungiyar Tarayyar Turai ta ci kamfanin Google tara mafi tsanani a tarihin kafuwar kamfanin da ta kai Euro bilyan hudu da milyan 340, lamarin da ake ganin zai kara tsamin dangantaka tsakanin Amurka da yankin Turai.
Wallafawa ranar:
Kungiyar Turai ta sanar da wannan tara ce sakamakon abin da ta kira yin amfani da hanyoyin da suka saba wa ka’ida wajen sanya kangi da kuma takura wa jama’a da ke amfani da Android domin gudanar da bincike-bincike da sauran abubuwa da ke samar wa kamfanin makudan kudade.
Kwamishinar Sashen bai wa Kamfanoni damar yin gasa da juna a fagen kasuwanci a kungiyar ta Turai Margrethe Vestager, ta ce kamfanin da ke Amurka na cin ribar sama da Euro bilyan 95 a shekara ta hanyar tallace-tallace da ke bayyana lokacin da jama’a ke amfani da man hajarsa ta bincike dangin smartphones, to amma yana boye gaskiyar abin da yake samu.
Ko baya ga wannan tara ta Euro bilyan 4 da milyan 340 wadda ta kai kashi 10% na jarinsa, Kungiyar ta Turai ta kuma bukaci Google ya dakatar da wannan yaudara cikin kwanaki 90 ko kuma ya fuskanci sabbin matakai.
A 2017, kungiyar ta samu kamfanin da laifi, in da ta dora masa biyan tarar Euro bilyan 2 da milyan 400, to sai dai a wannan karo kamfanin na Google ya ce zai daukaka kara a game da wannan tara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu