Isa ga babban shafi
Turai-Afrika

Harkar noma za ta samu tawaya a Turai

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ya bayyana cewar za a samu koma-baya a harkar noma a kasashen Turai nan da shekaru goma masu zuwa, yayin da aikin noman zai habaka a kasashen Afirka da Asiya.

Harkar noma za ta samu koma-baya a kasashen Turai, yayin da za ta habbaka a nahiyar Afrika kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya na nuna
Harkar noma za ta samu koma-baya a kasashen Turai, yayin da za ta habbaka a nahiyar Afrika kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya na nuna Zoé Berri
Talla

Binciken da Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar tare da hadin gwiwar Kungiyar Tattalin Arzikin Turai ya ce, rashin zaman lafiyar da ta mamaye Gabas ta Tsakiya da matsalar sauyin yanayi da kuma rashin ingantacciyar hanyar samar da abinci za su taimaka wajen matsalar da za a fuskanta a yankin.

Rahotan ya ce, a shekaru 10 masu zuwa hankali zai karkata ne wajen samun karin gonakin da ake nomawa domin samar da abinci a kasashe masu tasowa, yayin da za a samu akasin haka a kasashen da suka ci gaba, musamman yammacin Turai, in da ake hasashen samun habakar noma da samar da kifi da kashi 3 kacal.

Rahotan hadin gwiwar ya ce,  za a samu habakar kashi 30 na noman da ake yi a yankin Afrika da ke Kudu da Sahara, yayin da samar da nama da nonon shanu zai karu da kashi 25.

Sai dai duk da haka, rahotan ya ce, yankin zai ci gaba da dogara ga kasashen duniya wajen samun isasshen abincin da zai wadata shi, duk da habakar da za a samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.