Turai
Tarayyar Turai za ta bayar da kariya ga kananan Manoma
Kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar da wani shirin kare kananan manoman da ke yankin daga manyan Yan kasuwar da ke saye amfanin gonakin su domin samun kazamar riba.
Wallafawa ranar:
Talla
Kungiyar ta bayyana shirin samar da wani yanayi mai kyau, wanda zai bai wa bangarorin biyu damar gudanar da cinikin a tsakanin su ba tare da wani bangare ya yaudari wani ba.
Kwamishinan kula da bangaren noma a kungiyar, Phil Hogan, ya ce shirin wata dama ce wajen karfafa manoman domin ba su damar amfana da gumin da su ke zubar wa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu