Isa ga babban shafi
Amurka

Tilas Trump ya sake sada yara da iyayensu-Kotu

Wani alkali a Amurka ya bai wa gwamnatin kasar wa’adin kwanaki 30 da ta sake sada Iyaye da ‘ya’yansu da ta raba a lokacin da suka shiga kasar ta kan iyakarta da Mexico.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump 路透社。
Talla

A karkashin umarnin alkalin kotun da ke San Diego a Jihar California, tilas gwamnatin Donald Trump ta sake sada Iyaye da ‘ya’yansu masu kasa da shekaru 5 cikin kwanaki 14, yayin da kuma yara masu shekaru sama da 5, tilas a sake sada su da iyayensu cikin wa’adin kwanaki 30.

Tuni dai wasu karin jihohi 17 suka garzaya kotu don kalubalantar shirin na gwamnatin Trump da ke raba baki iyaye da ‘ya‘yansu da suka shiga kasar ta kan iyakarta da Mexico, cikinsu kuwa har da Washington da New York da Oregon da Pennsylvania.

Sama da kananan yara baki 1 da 100 ne aka raba da iyayayensu, kama daga watan Mayu zuwa yanzu, a karkashin shirin gwamnatin Donald Trump kan bakin-haure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.