Isa ga babban shafi
Amurka

Ni ba mai nuna wariyar launi ba ne-Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, shi ba mai nuna wariyar launin fata ba ne bayan kalamansa na kaskanci kan nahiyar Afrika sun janyo ma sa caccaka daga sassan duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A yayin zantawa da manema labarai a jiya Lahadi, shugaba Trump ya ce, “ ni ba mai nuna wariyar launi ba ne, nine mutum mafi sassaucin nuna wariya da kuka tana hira da shi”.

A karon farko kenan da shugaban ke mayar da martani kai tsaye game da zarge-zargen nuna wariyar launin fata.

Kafafen yada labaran Amurka sun rawaito cewa, shugaban ya furta kalaman wulakancin ne kan Afrika a yayin ganawa da mambobin majalisar dokokin Amurka a ranar Alhamis kan batun shige da fice a kasar.

Tuni Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Afrika suka yi tir da kalaman Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.