Isa ga babban shafi
Amurka-korea ta Arewa

Donald Trump ya kammala shirin ganawa da Shugaban Koriya ta Arewa

A yayin da ya rage kwanaki 5 a gudanar da tattaunawar sulhu tsakanin shugaban kasar Korea ta Arewa da Donald Trump na Amurka, shugaban Trump ya bayyana cewar yanzu sun shirya tsaf domin ganin zuwan ranar da aka shata.Trump ya  fadi hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin Firaministan Japan Shinzo Abe a fadarsa ta white house da ke a Washington DC.

Firaministan Japan Shinzo Abe da Shugaban Amurka Donald Trump
Firaministan Japan Shinzo Abe da Shugaban Amurka Donald Trump 路透社
Talla

Hasashen farko da aka yi cewar haduwar shugaba Trump da Kim na Korea ta Arewa mai yuwa ganawar tasu ta kasance a kan takarda ne, kasar Japan ke ta kara nanatawa cewar bai kamata Amurka ta yi saku-saku da batun ba.

Wannan ne karo na biyu da Shinzo Abe ke yin takakkiya zuwa Washington domin ganawa da shugaba Trump a kan wannan batun cikin watanni 2, kuma shinzo Abe na kara matsa kaimi ne domin ganin ba’a samu matsala a batun na dakatar da yaduwar makaman kare dangi a yankin na Korea ba.

Abe dai a ziyarar da ya kai Amurka ya shata wa shugaban kasar Amurka siradan da ya kamata ya bi wajen gamsar da shugaba Kim da mutane da dama ke gani a matsayin shu’umin mutum.

Yanzu haka dai ana da kwanaki kasa da 5 a gudanar da tattaunawar da kusan duk hankalin Duniya ya karkata akan sa, sai dai batun har yanzu na a zaman mace mai ciki , Allah dai ya san abinda za ta haifa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.