Isa ga babban shafi
Yemen

Mutane da dama ne suka mutu a yakin Yemen

Hukumomin Lafiya a kasar Yemen sun ce sojojin da masu tada kayar baya sama da 100 aka kashe a fafatawar da aka kwashe mako guda ana yi domin karbe iko da tashar jiragen ruwan kasar.

Tashar Jiragen ruwan Aden na kasar Yemen
Tashar Jiragen ruwan Aden na kasar Yemen © Murielle Paradon
Talla

Dakarun Yemen na kokowar ganin sun mamaye tashar jiragen ruwa da ake amfani da ita wajen kai kayan agaji ga mutane akalla miliyan 22 dake cikin halin kuncin rayuwa.

Masu aikin kula da lafiya a Kudancin Aden sun ce sun karbi gawarwakin mutane 52 da aka kashe cikin su harda sojoji 20 daga jiya zuwa yau, abinda ya kawo adadin mutanen da aka kasha zuwa 110.

Suma yan tawayen sun rasa mutane da dama a fafatawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.