Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra’ila ta kaddamar da sabon harin sama a kan kungiyar Hamas ta Gaza

A yau Alhamis kasar Isra’ila ta bayyana kai sabon farmakin sama ga wasu abubuwa mallakar kungiyar Hamas ta zirin Gaza, bayan abin da ta kira harin harbi da Bindiga da aka kai wa Dakarunta tare da lalata wani gini.

Wani harin da Isra'ila ta kai wa Gaza
Wani harin da Isra'ila ta kai wa Gaza REUTERS/Mohammed Salem
Talla

Dakarun kasar Isra’ila dai sun bayyana cewar sun kai harin ne ga mayakan kungiyar Hamas da ke a yankin na zirin Gaza inda harin ya lalata wasu kadarori mallakar kungiyar Hamas, da kuma wata Cibiyar kera makamai ta kungiyar Hamas.

Majiyar tsaro ta Falasdinu ta tabbatar da cewar an yi niyyar kai harin ne ga sansanin kungiyar Hamas, kuma ya zuwa yanzu babu bayannai akan ko an samu wadanda suka jikkata.

Ko a ranar Laraba ma kasar Isra’ila ta harba makamai ga wasu wurare uku na kungiyar Hamas bayan da aka samu rahoton harbi daga Gaza inda suka yi nasarar lalata wani gini a Isra’ila.

Musayar Wutar da ake tsakanin kungiyar Hamas da kuma Dakarun Isra’ilar dai ya biyo ne bayan wasu makonni da aka shafe ana zanga-zangar kyamar Isra’ila da Amurka, sakamakon maido da Ofishin Jekadancin Amurka a birnin Kudus daga birnin Tel Aviv na Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.