Isa ga babban shafi
Isra'ila

Kasashen duniya sun yi tir da kisan Falasdinawa 59

Kasashen duniya na ci gaba da Allah-wadai da Isra'ila kan kisan da sojojinta suka yi wa Falasdinawa 59 da ke zanga-zangar lumana ba tare da makami ba a Gaza, lokacin da Amurka ke bude sabon ofishin Jakadancinta a birnin Kudus.

Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 50 da ke zanga-zangar lumana a Gaza
Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 50 da ke zanga-zangar lumana a Gaza REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

Kasashe da dama cikinsu har da Birtaniya da Faransa da Rasha sun ki goyan bayan shirin mayar da ofishin Jakadancin na Amurkar zuwa birnin Kudus, yayin da wasu 128 a karkashin Majalisar Dinkin Duniya suka yi Allah-wadai da yadda Amurka ta bayyana Kudus a matsayin cibiyar Isra'ila.

Cikin kasashen da suka nuna bacin ransu kan kisan na jiya har da Afrika ta Kudu wadda ta janye Jakadanta da ke Isra'ila.

Ita ma dai Saudiya wadda abokiyar kawancen Amurka ce, ta ce ba ta ji dadin ganin yadda sojin Isra'illa ke kisan Falasdinawan ba, tare da bayyana bukatar kasashen duniya su yi wani abu domin dakatar da kisan bayin Allah.

Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riad Mansoor ya ce, suna tattaunawa a tsakaninsu wajen kiran taron gaggawa da zai yi Allah wadai da kisan.

A bangare guda, yau ne Falasdinawa ke shirin gangamin cika shekaru 70 da kwace musu filaye da kuma raba su da matsugunansu da Israila ta yi a shekarar 1948 da suka yiwa lakabi da Nakba wato 'Bala'i, abin da ya tilasta wa dubbansu tserewa daga yankin baki daya.

Yau ne kuma ake saran jana’izar mutanen da sojojin na Isra'ila suka kashe a lokacin zanga- zangar ta jiya .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.