Yan sanda Rasha sun kama Akexei Navalny
Yan Sanda a Rasha sun kama shugaban yan adawar kasar Akexei Navalny tare da dimbin magoya bayan sa da suka shiga wata zanga zangar adawa da shugaba Vladimir Putin da ake saran rantsar da shi sabon wa’adi na hudu gobe lahadi.
Wallafawa ranar:
Navalny wanda hukumar zabe ta haramtawa takara domin kalubalantar shugaba Putin yayi kira ga magoya bayan sa da yau su kaddamar da zanga zangar lumana domin nuna rahsin amincewar su da zaben.
Rahotanni sun ce cikin mutane 15 da aka tsare a yankin Siberia harda wani dan jarida, yayin da aka tsare 18 a Novokuznetsk.
Hukumomin kasar sun hana zanga zangar a Moscow da Saint Petersberg.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu