Isa ga babban shafi
Armenia

Al'ummar Armenia na bikin murnar murabus din shugabansu

Al’ummar kasar Armenia na ci gaba da bukukuwan jin dadi bayan da shugaban kasar ya bayyana sauka daga mukaminsa. Shugaba Serzh Sarkisian dai ya bayyana ajiye mukamin ne, lura da yadda mutanen kasar suka fantsama akan tituna suna zanga-zanga.

Al'ummar Armenia na bikin jin dadi saboda shugaban kasar ya yi murabus daga kujerarsa
Al'ummar Armenia na bikin jin dadi saboda shugaban kasar ya yi murabus daga kujerarsa REUTERS/Vahram Baghdasaryan/Photolure
Talla

Zanga-zangar da ta kai shuagaban ga ajiye kwallon mangoro domin ya huta da Kuda, ta samo asali ne daga batun nada shugaban a matsayin Firaminista da Majalisar kasar ta yi bayan kuma ya kwashe shekaru aru-aru bisa mulki a kasar wadda abokiyar kawancen kasar Rasha ce.

‘Yan adawa  ne suka yiwo ca..! akan zargin shugaban da kokarin kara wa’adin zaman bake-bake akan karagar mulkin kasar mai akalla mutane miliyan 300.

Dubban mutane sun harzuka suka kuma fantsama akan tituna suna kalaman Allah-wadai ga shugaban a babban birnin kasar na Yerevan da kuma wasu birane da dama.

Daga bisani dai shugaba Serkisian mai shekaru 63 ya bayyana wa al’ummar kasar dai bai yi daidai ba, don haka ya ce ga abinku.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutarres ya bukaci a mutunta ‘yancin Dimokradiyya da kuma hakkin fadar albarkacin baki, bayan wata zanga-zangar da ta yi sanadin saukar shugaban kasar Serzh Sarkisian.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.