Isa ga babban shafi
Armenia

Shekaru 100 da kisan kiyashi a Armeniya

Manyan shugabannin kasashen duniya da suka hada da Francois Hollande na Faransa da Vladimir Putin na Rasha sun halarci Yerevan babban birnin kasar Armenia domin bikin cika shekaru 100 da juyayin kisan kiyashin da aka yi wa Armeniyawa a zamanin yakin duniya na farko.

Shekaru 100 da kisan kiyashin da aka taba yi wa Arminiyawa akalla miliyan guda da rabi a zamanin daular Ottomaniya.
Shekaru 100 da kisan kiyashin da aka taba yi wa Arminiyawa akalla miliyan guda da rabi a zamanin daular Ottomaniya. REUTERS
Talla

Mujami’u a Armenia sun bukaci gudanar da addu’o’I na musamma a yau Juma’a, da aka cika shekaru 100 da kisan kiyashin da aka taba yi wa Arminiyawa akalla miliyan guda da rabi a zamanin daular Ottomaniya, farko yakin duniya na farko.

Shugaban kasar Armenia Serzh Sarkisian da wasu shugabanni da suka halarci bikin sun ajiye faranni a Yerevan domin karrama dubban mutanen da dakarun daular Ottoman suka kashe tsakanin 1915 zuwa 1917.

Bikin na zuwa ne yayin da kasashen yammaci ke ci gaba da matsawa Turkiya ta karbi laifin kisan na Armeniyawan, zargin kullum ta ke musantawa.

Za a shafe tsawon sa’o’I 2, ana gudanar da addu’o’I a harabar babbar mujami’ar birnin Yerevan kamar yadda hukumomin kasar suka sanar.

Kasar Armenia za ta ci gaba da juyayin kisan da aka yi wa mutanenta a wani lamari da ta bayyana mafi muni kuma na bakin ciki a tarihin kasar.

Armenia da a baya ke cikin Tarayya Soviet ta jima tana fafutukar neman hakkinta dangane da abin da ya faru karkashin jagorancin Daular Ottamaniya.

Armenia ta ce wata rana gaskiya za ta yi halinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.