Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ba shi da nagartar jagorancin Amurka- Comey

Tsohon daraktan Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI, James Comey ya ce, shugaba Donald Trump ba shi da nagartar rike ofishin shugaban kasa, yayin da ya bayyana shi a matsayin makaryacin da ke gurbata makusantansa.

Shugaban Amurka Donald Trump tare da  James Comey, tsohon shugaban Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump tare da James Comey, tsohon shugaban Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka REUTERS
Talla

A wata hira da aka yi da a  tashar talabijin ta  ABC, Comey ya ce bai damu da bayanan da ke cewar, Trump na fama da tabin hankali ko kuma ya fara shiga shekarun mantuwa ba, amma abin da ya sani shi ne, shugaban ba shi da nagartar rike ofishin shugaban kasa.

Comey ya kuma bayyana Mr. Trump a matsayin mutumin da ya mayar da mata tamkar "yankakkun nama".

Comey ya ce, ya dace shugaban Amurka ya zama kamili da ke mutunta muradun kasar da suka hada da gaskiya, amma ya ce, Trump ya rasa wadannan dabi'u.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da Comey ke shirin kaddamar da littafinsa mai suna " A Higher Loyalty: Truth, Lies and Leadership" a gobe Talata, in da ya yi bayani game da irin huldar da ya yi da Trump.

A shekarar da ta gabata ne Trump ya kori Comey daga mukaminsa, kuma a karon farko kenan da tsohon darektan na FBI ke magana a wata kafar talabijin tun bayan tsige shi a bara.

Bayan watsa hirar ta Comey, shugaba Trump ya aike da sakwanni ta shafinsa na  Twitter, yana bayyana Comey a matsayin makaryaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.