Rudani a fadar White House ta Amurka
Ana cikin rudani a fadar White House ta Amurka bayan da hukumar FBI ta kwace kayan nadar bayanai na dadadden Lauyar shugaba Donald Trupm Micheal Cohen.
Wallafawa ranar:
Hukumar leken asirin kasar Amurka FBI, ta ruwaito cewar Michael Cohen ya kasance mai nadar daukacin hirarrakin da yake yi ta Waya tsakaninsa da shugaba Donald Trump, kuma jami'ai a ofishin Lauyan na fargabar cewar da wuya hukumar FBI bata karbe hatta hirarrakin da Cohen ke yi da shugaba Trump ba.
FBI dai ta dade tana bibiyar sakwannin email da Cohen ke aikawa wurare daban daban a wani bangare na binciken yadda ya ke gudanar da harkar neman kudadeensa.
A baya dai an ga yadda ya biya Dalar Amurka Miliyan 1 da dubu 600 ga wata mata ta kamfanin gwajin kyau na Play Boy domin ta fake masa sirrin jima’i da ta yi da babbar mai samar da kudade ta Jam’iyyar Republican kuma makusanciyar shugaba Donald Trump.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu