Isa ga babban shafi
Libya

Yakin Libya ya haddasa bazuwar makamai a Duniya

Wani rahoton bincike na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa yakin basasar Libya  don hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Ghaddafi ne ya taimaka wajen yaduwar makamai a wasu kasashen duniya. Rahoton ya ce kasashen da makaman suka bazu sun hadar da Jamhuriyar Nijar da Somalia da Gaza da Falasdinu da kuma Syria.

Wani mayakin Libya dake marawa gwamnati baya  yayin fafatawa ma mayakan al sis a yankin Sirte na Kasar Libya
Wani mayakin Libya dake marawa gwamnati baya yayin fafatawa ma mayakan al sis a yankin Sirte na Kasar Libya Reuters
Talla

Rahoton ya kuma bayyana cewa tun a wancan lokaci an gargadi Hukumomin kasar cewar akwai yiwuwar yaduwar makaman musamman la'akari da yadda su ke bayar da su ga al'umma don tsoron fadawa a hannun masu tayar da zaune tsaye.

Rahoton ya ce ko a lokacin da aka kama wasu 'yan tawaye masu alaka da kungiyar al-Qaeda a yankin kudancin Algeria, an ga wasu daga cikin makaman da aka yi amannar cewar sun fito ne daga kasar ta Libya.

Shi dai wannan sabon rahoto na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniyar, ya ci gaba da cewar makaman sun yadu a wani matsayin da ba'ayi tsammani ba, domin ko a kasar Masar angano wadannan makamai, da ake kyautata zaton cewar da su ake amfani a yankin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.