Faransa ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta dau mataki kan Libya
KASAR Faransa ta ce ya zama wajibi Majalisar Dinkin Duniya ta dauki mataki mai tsauri kan kasar Libya domin kawo karshen cinikin bayin da ake samu a kasar. Tun bayan gano badakalar cinikin bayin a Libyan Faransa ke ci gaba da nuna rashin jin dadi tare da yin Tir da batun.
Wallafawa ranar:
Jakadan Faransa a Majalisar Francois Delattre ya bayyana haka kafin taron da kasar sa ta kira na kwamitin Sulhu yau talata domin tattauna matsalar.
Delattre yace ya zama dole Majalisar ta zarce Magana ta fatar baki wajen daukar mataki a aikace kan wannan mummunar matsala da aka samu.
Jakadan ya shaidawa manema labarai a birnin New York cewar bai kauda shakkun sanyawa kasar takunkumi ba saboda girmar matsalar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu