Isa ga babban shafi
Algeria

Mutane 257 sun mutu a hatsarin jirgin saman soji a Algeria

Mutane 257 sun rasa rayukansu bayan jirgin sojin da ke dauke da su ya yi hatsari  jim kadan da tashinsa daga wani sansani da ke kusa da babban birnin kasar Algeria, kuma akasarin fasinjojin sojoji ne da iyalansu.

Jirgin sojin Algeria da ya yi hatsari dauke da mutane 257
Jirgin sojin Algeria da ya yi hatsari dauke da mutane 257 ENNAHAR TV/Handout/ via REUTERS
Talla

Daga cikin mamatan akwai mutanen yankin Polisario 26 da ke samun goyon bayan gwamnatin Algeria wajen neman 'yancin cin gashin kai a yammacin Sahara daga Morocco.

Ma'aikatar tsaron Algeria ta tabbatar da mutuwar daukacin fasinjojin ba tare da samun mutun guda da ya tsira da ransa ba.

Mataimakin Ministan tsaron kasar, Janar Ahmed Gaid Salah da ya ziyarci yankin da lamarin ya faru, ya bukaci guanar da bincike kan hatsarin.

Wani dan jarida da ke daukar hoto a karkashin Kamfanin Dillacin Labaran Faransa  AFP ya rawaito cewa, bakin hayaki mai kauri na ci gaba da tashi a wurin da hatsarin ya auku.

Tuni daruruwan motocin daukar mara lafiya da manyan motocin kashe gobara suka  kama hanyar isa wurin da lamarin ya faru.

Ba a karon farko kenan ba da ake samun mummunan hatsarin jirgin sama a Algeria, in da ko a cikin watan Fabairun 2014, sai da mutane 77 suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin saman soji a yankin kudancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.