Isa ga babban shafi
facebook

Shugaban Facebook na shan matsin lamba

Shugabannin Kasashen Turai na shirin matsin lamba ga manyan kamfanonin fasahar sadarwa don kare bayanan sirrin jama’ar da ke amfani da su. Wannan na zuwa ne a yayin da wata badakalar tatsar bayanan sirri ta ritsa da kamfanin Facebook duk da cewa, shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg ya bada hakuri.

Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg
Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg REUTERS/Stephen Lam
Talla

Kungiyar Tarayyar Turai na shirin daukan matakin magance matsalar tatsar bayanan miliyoyin mutane a dandalin sada zumunta na Facebook da wani kamfanin Birtaniya, Cambridge Analytica ya yi, abin da ya taka rawa a yakin neman zaben shugaban Amurka Donald Trump a shekarar 2016.

Wata sanarwa da Kungiyar ta EU ta fitar a wannan Alhamis ta ce, akwai bukatar kamfanonin sada zumunta ta yanar gizo su tabbatar da kare bayanan sirri na jama’a.

Ko da dai shugaban na Facebook, Mark Zuckerberg ya fito ya bada hakuri game da wannan matsalar, in da ya ce, "wannan wani babban cin amana ne, amma ina matukar bada hakuri kan abinda ya faru. Matukar dai muna da alhakin kare bayanan jama’a, amma muka gaza yin haka, to lallai ba mu cancanci yi wa jama’a hidima ba.To amma, aikin da ke gabanmu a yanzu, shi ne tabbatar da cewa, hakan bai sake faruwa ba."

Tuni Majalisar Dokokin Amurka ta bukaci Zuckerberg da ya yi bayani kan wannan badakala, yayin da hukumomin Isra’ila a yau suka ce, sun kaddamar da bincike kan ayyukan Facebook saboda wannan al’amari da ya girgiza kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.