Isa ga babban shafi
Syria

MDD za ta shigar da kayan agaji yau a Ghouta na Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta kammala shirye-shiryen shigar da isassun kayayyaki a yankin gabashin garin Ghouta na Syria yau Litinin.Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da manyan kasashen duniya ke kara matsa kaimi ga makusantan gwamnatin Syria wajen ganin sun taimaka don kawo karshen kashe daruruwan fararen hula a Ghouta.

Kananan yara na cikin halin kunci a yankin gabashin Ghouta saboda hare-haren dakarun gwamnatin Syria
Kananan yara na cikin halin kunci a yankin gabashin Ghouta saboda hare-haren dakarun gwamnatin Syria REUTERS/Bassam Khabieh
Talla

Majalisar ta ce, tawagarta ta jami’an jinkai sun shirya tsaf don shigar da kayayyakin agajin kowanne lokaci daga yanzu, duk da luguden wutar dakarun gwamnati don kakkabe ‘yan tawaye a garin.

Majalisar ta ce, akwai tarin manyan motoci 46 makare da abinci, magunguna da ma sauran kayan bukata da zai wadaci akalla mutane dubu 27 da 500.

Mai kula da shirin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Syria, Ali al-Za'atari ya ce, suna fatan ilahirin motocin wadanda za su tafi cikin jerin gwano, su samu damar kai wa yankin na gabashin Ghouta ba tare da tangarda ba.

Manyan kasashen duniya ciki har da Amurka da Faransa sun ci gaba da lallamar kasashen da ke kawance da shugaba Bashar al assad wajen ganin ya tsagaita  luguden wutar da yake yi a yankin na gabashin Ghouta da ke fuskantar kawanya tun a shekarar 2013, yayin da mutane fiye da dubu 400 ke bukatar kulawar lafiya da abinci.

Shugaban Fransa Emmanuel Macron ya bukaci takwaransa na Iran Hassan Rouhani ya yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an kawo karshen luguden wuta a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.