Yawan wadanda suka hallaka a gabashin Ghouta ya zarta 670
Jami’an agaji a Syria, sun ce zuwa yanzu hare-haren da jiragen yakin sojin kasar ke ci gaba da kai wa kan yankin Gabashin Ghouta ya hallaka sama da fararen hula 674 acikin mako guda.
Wallafawa ranar:
Farmakin kan yankin ‘yan tawayen na ci gaba da gudana ne, duk da cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar tsagaita wutar yakin Syria a ilahirin kasar tsawon kwanaki 30.
Daga cikin fararen hular da suka hallaka akwai kananan yara 22 da mata 43.
A wani labarin kuma, fararen hular da ke zaune a yankin sun ki amincewa da tayin ficewa da gabashin na Ghouta, a karkashin tsarin tgaita wuta a tsawon awanni 5 a kullum da Rasha ta gabatar.
Fararen hular sun bayyana dalilinsu da cewa basu da tabbacin tsare rayukansu a lokacin da suka amsa tayin ficewa daga yankin.
Yankin Gabashin Ghouta mai yawan al’umma dubu 400,000, ya kasance a karkashin kawanyar sojin gwamnatin Syria tun a shekarar 2013, bayan kwace ikon yankin da ‘yan tawaye suka a tsakiyar shekarar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu