Majalisan Dinkin Duniya ta damu da makomar 'yan gudun hijirar Congo
Majalisar Dinkin Duniya ta sake gargadi cewar tabarbarewar al’amura a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo zai haifar da mummunar yanayi kan halin da yan gudun hijira zasu shiga.
Wallafawa ranar:
Hukumar da ke kula da Yan gudun hijira ta Majalisar ta ce Yankin Tanganyika na ci gaba da fuskantar mummunar tashin hankali, sakamakon barkewar fada da masu dauke da makamai suka kaddamar.
Mai magana da yawun hukumar, Andrei Mahecic, yace fafatawa tsakanin Yan Kabilar Bantu da Twa na ci gaba da haifar da matsaloli a kasar.
Jami’in yace sun samu rahotanni 800 da suka hada da kisa da sace mutane da kuma fyade a makwanni biyu na watan Fabarelun shekara 2018, abinda ke da matukar fargaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu