Isa ga babban shafi
Duniya

Guterres ya bukaci ci gaba da matsa lamba ga Korea ta Arewa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci shugabannin kasashen duniya su tashi tsaye wajen shawo kan wasu batutuwa da yanzu haka ke yiwa duniyar barazana.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Yayin jawabi wajen taron tsaro da ake gudanarwa a Munich da ke kasar Jamus, Guterres ya bayyana wadanan barazana da suka hada da yake-yake da makamin nukiliya da matsalar amfani da yanar gizo da makamashi da kuma tabbatar da lafiyar al’umma.

Da yake jawabi kan yadda dangantaka ke kara tsami tsakanin Amurka da Korea ta arewa, Guterres ya ce kamata ya yi kasashen biyu su zauna kan teburin sulhu don samar da maslaha wadda ya ce za ta amfani duniya baki daya.

A cewar sa rikici ba zai amfanar da kowanne bangare ba, face kara fargaba da zaman dar dar ga al'ummar kasashen, inda ya ce yana da yakinin Amurka na da niyyar tattaunawar, kuma kalaman mataimakin shugaban kasar na baya bayan nan ya tabbatar da hakan.

Guterres ya kuma bukaci ci gaba da matsa lamba ga Korea ta Arewan domin shawo kan wajen dakatar da barazanar gwaje-gwajen makaman nukiliyar, wanda ya ce yana jefa al'umma cikin tsoro.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya kuma bukaci hada hannu tsakanin kasashen duniya don kawo karshen yake-yaken da ke ci gaba da sabbaba salwantar rayukan mutanen da basu-ji-basu gani ba musamman a yankin gabas ta tsakiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.