Iran ta tabbatar da hannun Amurka da Saudiyya a zanga-zangar kasar
Babban mai shigar da kara a Iran ya ce jami’an leken asiri na CIA ne suka taka muhimmiyar rawa wajen assasa zanga-zangar da kasar ta fuskanta a baya-bayan nan wanda kuma suka samu goyon bayan kasashen Isra’ila da Saudiyya. Tun da farko dama Iran ta zargi kasashen Amurka da Saudiyya da hannu wajen tunzura masu zanga-zangar.
Wallafawa ranar:
Kamfanin dillacin labaran Iran IRNA ya ruwaito Mohammad Jafar Montazeri na cewa kasashen na Amurka da Saudiyya da kuma Isra’ila sun kai fiye da shekaru 4 suna shirye-shiryen zanga-zangar don tayar da hankali a Iran.
A cewar Mohammad Montazeri wani bincike da hukumar sirri ta Iran ta gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa kasashen sun yi amfani jami’an tsaron leken asirin CIA wajen tunzura masu zanga-zangar.
A cewar Montazeri, jami’an tsaron CIA na Amurka da na Mossad da ke Isra’ila su ne suka taka muhimmiyar rawa a zanga-zangar yayinda Sa’udiyya kuma ta biya dukkanin kudaden da ake bukata.
Duk da yake gwamnatin Amurka ta musanta hannu a zanga-zangar amma Iran ta ce tana kwararan hujjoji da ke nuna kasashen uku sun taka muhimmiyar rawa wajen shiryawa dama ingiza masu zanga-zangar.
Akalla mutane 22 ne suka mutu yayinda aka kame fiye da mutane 450 yayin zanga-zangar kan matsin rayuwa a Iran wadda ta faro daga ranar 28 ga watan Disamban shekarar 2017.
Zanga-zangar dai ita ce irinta mafi muni da Iran ta taba fuskanta tun bayan ta shekarar 2009.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu