Isa ga babban shafi

'Matan da suka fallasa cin zarafi ne gwarzon shekara ta 2017'

Mujallar New York Times ta Amurka ta bayyana Matan da suka fallasa cin zarafin da suka fuskanta a masana’antar Hollywood a matsayin gwarzon Shekara ta 2017.

Matan da suka fallasa cin zarafinsu ne gwarzon Mujallar Time
Matan da suka fallasa cin zarafinsu ne gwarzon Mujallar Time Time Inc./Handout
Talla

Har illa yau Jaridar ta bayyana Shugaban Amurka, Donald Trump a matsayin na biyu sai Xi Jinping na China a matsayin na Uku.

Matan da Mujallar New York Times ta bayyana a matsayin ‘masu fasa kwai’ su ne gwarzon shekara ta 2017.

Matan sun kunshi fitattun jaruman fina-finan da suka fito fili suka fallasa cin zarafi da lalata da suka fuskantar daga wajen fitaccen mai shirya fina-finan Hollywood, Harvey Weinstein.

Lamarin dai ya kai ga kirkira alamar #Metoo wato ‘nima’ wajen bayanan labarai iri-iri na cin zarafi da Fyade da suka ce na faruwa a masanatar Hollywood.

Wannan batu da Weinstein ya Musanta ya bayyana abubuwa da dama da ke faruwa tsakanin hamshakan Hollywood da manyan ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da kafafan yadda labarai.

Fitattun jarumai mata irinsu Ashley Judd da Angelina Jolie na cikin Jarumai mata fiye da 40 da suka fito fili suka bayyana cewa Weinstein ya yi lalata da su tun lokacin da mujallar Times ta soma kwarmata batun.

Tun a shekara ta 1927 Mujallar Times ke ware mutum ko kungiyar da ta shara a cikin shekarar a matsayin gwarzon shekarar.

A shekara ta 2015 Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ce gwarzuwar shekara saboda girman bakin da suka kwarara kasarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.