Isa ga babban shafi
RFI

Ranar yaki da cin zarafin ‘yan jaridu ta duniya

Yau ne ake bikin ranar yaki da yadda ake cin zarafin ‘yan Jaridu ta duniya, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakar da mutane muhimmancin aikin Jaridu da kuma basu kariyar da ta dace.

Babbar Daraktar RFI Cécile Mégie
Babbar Daraktar RFI Cécile Mégie RFI/Pierre René-Worms
Talla

Wannan rana ta biyo bayan kisan da aka yiwa wasu 'yan jaridun Radio France Internationale guda biyu a Mali, Ghislane Dupont da Claude Verlon.

Tuni RFI ta kaddamar da wani shiri domin horar da matasan aikin Jarida a karkashin sunayen wadannan 'yan jaridu da aka yiwa kisan gilla.

Wannan ne karo na hudu da za a bayar da wannan dama ga dan jarida daya da kuma jami’in daukar sautin rediyo daga kasashen Afrika renon Faransa.

Mahalarta bikin da ake gudanar a birnin Dakar na Senegal sun hada da Marie-Christine Saragosse shugabar kafafen yada labaran Faransa da ke watsa shirye-shirye zuwa ketare, da Cécile Mégie babbar Darakatar rfi, da kuma ‘yan uwa da dangin Ghislaine Dupont da Claude Verlon.

Taron ranar yaki da cin zarafin 'yan jaridu na RFI a birnin Dakar na Senegal

A Karon farko dai an sanar da sakamakon gasar ne a kasar Mali, sai na biyu a Madagascar yayin da a bara aka sanar da sakamakon a Jamhuriyar Benin.

Ana dai gudanar bikin ne a wannan rana da aka kebe domin kawo karshen cin zarafin ‘yan jarida a duniya.

A shekara ta 2014 aka kashe ma’aikatan na RFI, a kusa da garin Kidal na arewacin Mali, a dai-dai lokacin da suke gudanar aikinsu.

A dai-dai lokacin da aka cika shekaru hudu da faruwar wannan lamari ne aka samu bayanan da ke tabbatar da cewa biyu daga cikin mutane Ukun da ake zargi da aikata kisan na zaune ne a cikin kasar Algeria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.