Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa- Amurka

Sojan Amurka Sun Kewaya Yankin Korea ta Arewa

Kasar Amurka ta ce wasu Dakarunta gwanayen jefa bama-bamai tare da rakiyar wasu jiragen yaki sun ratsa gaban tekun kasar Korea ta Arewa yau Asabar domin nuna mata irin karfin soja da  Amurka ta mallaka.

Shugaban Amurka Donald Trump  da takwaransa na Korea ta Arewa Kim Jong-un
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Korea ta Arewa Kim Jong-un rfi
Talla

Dana White  kakakin ma'aikatar Tsaro ta Amurka ta bayyana cewa kewayen da Dakarun Amurka suka yi don nuna karfin sojan da za su iya yin duk abinda ake so ne.

Ta bayyana cewa kasar Amurka na shirye domin amfani da karfin soji domin ganin ta kare gida Amurka da kawayenta.

A halinda ake ciki,  wasu bayanai na cewa an sami ‘yar girgizan kasa kusa da inda Korea ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami bada dadewa ba.

A wani labarin,  Ministan Waje na kasar Korea ta Arewa yau Asabar  a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya ya yi ta chachchakan Shugaban Amurka Donald Trump.

A lokacin da aka bashi dama domin jawabi Ministan Waje na Korea ta Arewan Ri Yong-Ho ya ce shugaban Amurka tababbe ne kuma mai son iyawa.

Ya bayyana cewa ikirarin da Donald Trump ya yi cewa zai daidaita Korea ta Arewa, ya sa suka kintsa rokokin su domin gano komi na sirrin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.