Isa ga babban shafi
china-amurka

China ta gargadi Trump kan Korea Ta Arewa

Shugaban China Xi Jinping ya bukaci takwaransa na Amurka Donald Trump da ya guje wa kalaman da ka iya rura rikicinsa da Korea Ta Arewa.

Yakin cacar-baka tsakanin Amurka da Korea Ta Arewa na neman tsananta
Yakin cacar-baka tsakanin Amurka da Korea Ta Arewa na neman tsananta REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da yakin cacakar-baka tsakanin bangarorin biyu ya janyo hankulan kasashen duniya, in da a baya-bayan nan shugaba Trump ya ce, gwamnatin Korea Ta Arewa za ta gane kuranta na fito na fito da Amurka.

A bangare guda, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nuna damuwa game da barazanar harba makamin Nukilya daga Korea Ta Arewa, in da ya ce, kasashen duniya na bukatar yin aiki tare don ganin cewa, kasar ta dawo kan turbar tattaunawar sulhu ba tare da gindaya wasu sharudda ba.

Gwaje-gwajen makaman Nukiliya da Korea Ta Arewa ta yi a 'yan kwanakin nan ya janyo ma ta suka daga kasashen duniya, yayin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake kakaba ma ta takunkumai masu tsauri a matsayin jan-kunne a gare ta.

Kazalika Korea Ta Arewan ta yi barazanar cilla makami mai linzami zuwa yankin Guam na Amurka da ke tsibirin tekun Pacific, lamarin da ya dada fusata shugaba Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.