Isa ga babban shafi
Venezuela

Venezuela: Amurka ta kakabawa Maduro takunkumi

Kasar Amurka ta sanar da sanyawa shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro takunkumi bayan ta yi watsi da sakamakon zaben wakilan majalisar kasar da aka gudanar a karshen mako da za su rubutawa kasar sabon kundin tsarin mulki.

Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela
Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela Miraflores Palace/Handout via REUTERS
Talla

Sai dai shugaba Maduro ya yaba da matakin wanda ya danganta a matsayin kin karbar umurni daga shugaban Amurka.

Kungiyar kasashen Turai da kasashen Colombia da Mexico da Peru sun bi sahun Amurka wajen kin amincewa da sakamakon zaben, yayin da Babbar lauyar Gwamnatin Venezuela Luisa Ortega ta bayyana zaben a matsayin haramtacce.

Amurka ta kira Nicolas Maduro a matsayin shugaban kama-karya, bayan ta rufe asusun ajiyarsa tare da haramtawa Amurkawa hulda da shi.

Sai dai kuma kasashe irinsu Rasha da Cuba da Bolivia na goyon bayan Maduro da ke fuskantar adawa da zanga-zangar kin jinin shi a Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.