Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya tube mai ba shi shawara kan sadarwa

Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami babban daraktan sadarwa a fadar white house Anthony Scaramucci duka kwanaki 10 bayan nada shi mukamin. Tube Scaramocci na zuwa ne bayan rantsar da sabon shugaban ma’aikata a fadar White House Janar John Kelly.

Scaramucci Daraktan sadarwa a fadar White House
Scaramucci Daraktan sadarwa a fadar White House REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Fadar white House dai ba ta bayyana cewa ko shugaba Trump ko kuma Kelly ne suka kori Scaramucci, amma alamu ya nuna dukkaninsu ba su bukatar ci gaba da aiki tare da shi.

Scaramucci dai ya janyo wa kansa bacin suna a fadar White House inda ya yi sanadin shugaban ma’aikata Reince Priebus da kakakin fadar white house Sean Spicer yin murabus.

Gwamnatin Trump dai ta fuskanci kalubale da dama da suka hada da sa’insa a fadar White House tsakanin ma’aikata da kuma kora da murabus din jami’an gwamnati da bincike da rashin samun biyan bukatu a majalisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.