An kammala taron kasashen G7 ba tare da matsaya ba kan dumamar yanayi
Shugabannin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki da masana'antu da ake kira G7 sun kammala taron su yau Asabar a Sicily na kasar Italiya da fatan ganin sun kare muradunsu, amma kuma sun ki tsaida matsaya dangane da batun dumamar yanayi.Bisa dukkan alamu dai an tashi wannan taro ba tare da cimma matsaya sosai ba kamar yadda ake so musamman game da dumamar yanayi.
Wallafawa ranar:
Shugabannin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki har sun kama hanyar tafiya kasashen su bayan kasashen ciki har da kasar Amurka sun amince su kara zafafa takunkumin da suka kakabawa kasar Rasha saboda matakin mallake yankin Crimea da Rasha ta yi.
Sanarwar bayan taron na shugabannin kasashen na cewa har sai Rasha ta nuna da gaske take yi wajen aiwatar da yarjejeniyar Minsk da kuma mutunta ‘yancin kasar Ukraine.
Sanarwar na yabawa kasar Ukraine da bata tabbacin samun hadin kan manyan kasashen duniyan masu karfin tattalin arziki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu