Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka-Turai

An soke taron G8 a Rasha da kuma maida shi na G7 a Brussels

Kasashen yammacin Duniya sun soke babban taron G8 na kasashe masu karfin tattalin arziki a Duniya da aka shirya gudanarwa a kasar Rasha. Wannan kuwa, da manufar kara kaifin matakan da suka dauka na maida Rasha Saniyar Ware akan rawar da ta taka a rikicin kasar Ukrain

simple.wikipedia.org
Talla

Bayan kammala wani taron tattaunawa na gagawa da shugban kasar Amurka barack Obama ya kira an bada sanarwar cewar yanzu an soke babban Taron kasashe masu karfin tattalin arziki a Duniya watau G8 da aka shata gudanarwa a birnin Sochin kasar Rasha a cikin watan Yuni.

Sanarwar hakama ta bayyana cewar an maye gurbin bagiren taron da aka bayyana da G7 da za’a yi a birnin Brussels, kuma sam ba za’a bari kasar Rasha samu halarta ba.

Hakama gamayyar kasashen na G7 kamar yanda suka bayyana kansu bayan fitar da kasar Rasha daga cikinsu, sun lashi Takobin kara kakabawa Rasha takunkumi akan shiga cikin rikicin Crimea

Tun daga farko dai sai da fadar White House ta Amurka ta bayyana damuwa ainun akan yanda Rasha ta jibge Dakarunta a kan iyakar kasar.

Sai dai wannan matakin da kasashen G7 suka dauka akan Rasha, ya janyo masu suka daga Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov harma yana mai cewar idan Kasashen na G8 na ganin tsantsame Rasha daga cikin su alkhairi ne, to su ci gaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.