Isa ga babban shafi
Amurka-Saudiya

Ta'addanci: Trump ya bukaci hadin kan kasashen Musulmi

Shugaban Amurka Donald Trump wanda ke gabatar jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya a birinin Riyad na kasar Saudiyya, ya bukaci kasashen musulmi da su kaucewa ba wadanda ake kallo a matsayin ‘yan ta’adda mafaka a kasashensu.

Shugaban Amurka Donald Trump yayin da yake gabatar da jawabi gaban taron Amurka da kasashen Muslmi a birnin Riyadh na Saudiya.
Shugaban Amurka Donald Trump yayin da yake gabatar da jawabi gaban taron Amurka da kasashen Muslmi a birnin Riyadh na Saudiya. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Trump ya ce Amurka na fatan yin aiki da sauran kasashen Musulmi domin yaki da ‘yan ta’adda, inda ya sanar da kulla kawance da kasashen yankin tekun Fasha, kan yadda za a hana ‘yan ta’addar samun kudade domin tafiyar da ayyukansu.

Akalla shugabanni ko kuma wakilansu daga kasashen Musulmi mafi rinjaye ne, suka halarci taron da ke cigaba da gudana a birnin Riyadh na Saudiyya.

A gefe guda kuma an cimma yarjejeniyar kulla alakar cinikayya tsakanin Saudiyya da Amurka, daya daga cikin yarjejeniyoyi mafi girma a tarihin kasar Amurka, kasancewar, jimillar kudaden da ke kunshe cikin yarjejeniyar ya kai Dala biliyan 110.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.