Yarjejeniyar ciniki tsakanin Amurka da Saudiya
Amurka da Saudiya sun kulla ‘yarjejeniya cinikin makamai da kudin su ya kai dalar Amurka biliyan 110 a ziyarar farko da Shugaban Amurka Donald Trump ya kai kasar.
Wallafawa ranar:
Wani jami’in Amurka ya ce yarjejeniyar ta hada da samar da kariya da sayar da makamai ga kasar Saudiya domin bada gudummuwarta wajen shawo kan ta’adanci a yankin gabas ta tsakiya.
Jami’in ya kara da cewa kasashen biyu na da kyaukkyawar alaka da ta shafi tsaro fiye da shekaru 70 da suka wuce.
Wannan ce dai ziyarar farko da Trump ya kai wata kasa tun bayan zama shugaban kasa watanni hudu da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu