Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta kashe sojojin Afghanistan 140

Mayakan Taliban sun kashe sojojin Afghanistan kimanin 140 a wasu jerin hare-hare da suka kaddamar musu a sansaninsu da ke yankin arewacin kasar a jiya Jumma’a.

Taliban ta kashe sojojin Afghanistan 140 a sansaninsu da ke Maza-r-Sharif
Taliban ta kashe sojojin Afghanistan 140 a sansaninsu da ke Maza-r-Sharif REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Wani Kwamandan sojin Amurka, Janar John Nicholson ya bayyana cewa, Taliban ta kai hare-haren ne kan sojojin da ke dawowa daga sallar jumma’a da kuma wadanda ke kalace a wani kanti cin abinci a sansanin

Sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar kashe 10 daga cikin mayakan a arangamar da suka shafe sa’oi a shalkwatar sojojin da ke birnin Mazar-i-Sharif.

Ma’aikatar tsaron kasar ta ce, mayakan sun kai harin ne sanye da kakin soji don bad-da-kama.

Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid ya ce, harin wani ramako don huce takaicin kisan da aka yi wa jiga-jigan kungiyar da dama a yankin arewacin Afghanistan.

Ana ganin wannan harin shi ne mafi muni da aka kai sansanin sojin kasar a tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.