Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar Dokokin Amurka za ta binciki alakar Trump da Rasha

Majalissar Dattijen Amurka ta kaddamar da bincike kan kutse da ake zargin Rasha da aikatawa a lokutan zaben kasar, inda ta ce rahotanni da ake ta yadawa kan Rasha da alakarsu da Trump abin damuwa ne da ya kamata a bincike gaskiya.

Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump
Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Bincike da ya samu goyon bayan Jam’iyyun siyasar kasar biyu na Democrats da Republican zai tabbatar da Sahihanci bayanan gwamnatin Obama mai barin gado ko akasin haka da kuma Donald Trump da ya ci zabe a ranar 8 ga watan Nuwamba.

Ana dai zargin Rasha da taka muhimmiyar rawa wajen Nasara Trump, zargin da fadar Kremlin ta Musanta.

Gwamnatin Obama ba ya ra'ayi Shugaba Putin na Rasha, sai dai Trump ya nuna alamar kulla alaka da kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.