Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya ce wani Arziki ne idan har Putin na kaunar shi

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ce wani babban arziki ne ace shugaban Rasha Vladimir Putin na kaunar shi, amma hakan ba zai zama dalilin kasancewarsu aminnan juna ba.

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump.
Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump. REUTERS
Talla

Trump ya fadi haka ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a karon farko tun lashe zaben shugaban kasa a watan Nuwamba.

Trump ya ce yana fatar yin tare da Putin amma kuma akwai alamun za su yi hannun riga.

Kalaman Trump dai na zuwa ne bayan bankwado wasu bayanan sirri akan shi da ake zargin aikin Rasha ne.

Trump ya yi watsi da rahoton wanda Kafar BuzzFeed da ke yada labarai a intanet a Amurka ta wallafa mai shafi 35 game da shugaban mai jiran gado. Amma ya amince Rasha ta yi shishshigi tare da yin kutse ga Jam'iyyar Democrat da 'Yan takararta Hillary Clinton.

Rahoton da BuzzFeed ta wallafa na kunshe ne da binciken da aka tattara akan Trump musamman lokacin da ya ke yakin neman zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.