Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya aminta da Rasha ta yi wa Amurka shishshigi a zabe

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, a karon farko ya amince da zargin da hukumar tara bayanan sirri ta kasar ke yi wa Rasha na yin shisshigi a lamurran zaben shugaban da ya dora shi kan karagar mulki.

Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump.
Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump. REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Reince Priebus, shugaban ma’aikata a fadar shugaban mai jiran gado, ya ce Trump ya amince da zargin, amma wannan ba ya nufin cewa ya amince kutsen na Rasha ne ya taimaka ya lashe zaben da aka gudanar a watan Nuwamba.

Trump ya dade yana yin watsi da zargin Rasha da yi kutse domin taimaka ma shi lashe zaben shugaban kasa, yana mai zargin sai idan China ce ta yi kutsen.

Binciken Jami’an leken asirin Amurka dai ya tabbatar da Rasha ta yi kutsen, matakin da ke ci gaba da matsin lamba ga Trump ya amince da laifin da ake tuhumar Rasha.

Amurka na zargin Rasha ne da yin kutse ga shafukan Jam’iyyar Democrat da Imel din ‘Yar takarar jam’iyyar Hillary Clinton da nufin dagula yakin neman zabenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.