Isa ga babban shafi
Amurka

Hukumar leken asirin Amurka na da hujjoji akan Rasha

Babban Jami’in hukumar leken asirin Amurka ya jaddada cewa akwai hujjoji da ke tabbatar da Rasha ta yi kutse ga sha’anin zaben shugaban kasa. Wannan kuma na zuwa duk da shugaba mai jiran gado Donald Trump ya ki amincewa da zargin da ake yi wa kasar ta Rasha.

James Clapper, daraktan hukumar leken asirin Amurka
James Clapper, daraktan hukumar leken asirin Amurka REUTERS
Talla

James Clapper ya shaidawa majalisar Dattijai cewa akwai kwararan hujjoji da bincikensu ya samu akan kutsen da Rasha ta yi wa zaben shugaban kasa.

Jami’in ya fadi haka ne kafin su gana da shugaba mai jiran gado Donald Trump kan batun kutsen na Rasha a zaben watan Nuwamba da aka gudanar.

Mista Clapper ya shaidawa majalisa cewa ba sabon abu ba ne ga Rasha na shiga sha’anin zaben wasu. Sannan Amurka ba ta taba ganin wani ya shiga sha’anin zabenta ba kamar yadda Rasha ta yi a bana.

A cewar babban jami’in leken asirin na Amurka, manyan Jami’an gwamnatin Rasha ne suka bayar da umurnin yin kutsen ga Jam’iyyar Democrat da kuma imel din Hillary Clinton, wadanda kuma aka mika wa Wikileaks domin kunyata jam’iyyar tare da dagula yakin neman zaben Clinton.

Amma Donlad Trump da ke shirin karbar mulki a 20 ga Janairu ya ta karyata zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.