Isa ga babban shafi
Amurka

''Dan bindigan Florida na iya fuskantar hukuncin Kisa''

Hukumomin Amurka za su tuhumi jami’in Sojin kasar da ake zargi da kai harin bindiga da ya lakume rayuka 5 a fillin jiragen saman Florida, laifin da ka iya fuskantar hukuncin kisa, yayin da ake ci gaba da bincike ko harin na da alaka da ayyukan ta’addanci.

Fasinjoji sun shiga rudani a lokacin harin bindiga a fillin jiragen saman Fort Lauderdale da ke Florida
Fasinjoji sun shiga rudani a lokacin harin bindiga a fillin jiragen saman Fort Lauderdale da ke Florida REUTERS/Andrew Innerarity
Talla

Babban alkalin Amurka Wifredo Ferrer a wata sanarwa ya ce idan aka samu dan bindiga mai suna Esteban Santiago da laifi to zai fuskanci hukunci kisa ko daurin rai da rai.

Santiago mai shekaru 26, ana zarginsa na kasha mutane 5 da jikkata wasu 6, bayan haifar da turmutsitsi tsakanin duban mutane da ke gudun neman tsira bayan harbe-harben bindiga a fillin jiragen sama Florida.

Hukumar FBI ta tsananta Bincike kan Santiago don sanin dalilan kai harin bindigan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.