Rikicin gidan yarin Brazil ya kashe mutane 60
Akalla mutane 60 sun rasa rayukansu bayan wata tarzoma ta barke tsakanin kungiyoyin ‘yan daba a wani gidan yarin Brazil, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar.
Wallafawa ranar:
Lamariin ya faru ne a jiya Lahadi a birnin Manaus na jihar Amazonas kamar yadda daya daga cikin masu kula da gidan yarin, Pedro Florencio ya shaida wa manema labarai.
Ko a cikin watan Oktoban da ya gabata, sai da aka samu irin wannan rikici tsakanin ‘yan daba a gidajen yarin kasar uku, abin da ya haddasa asarar rayukan jama’a da suka hada da wadanda aka kona da ransu.
Brazil na cikin kasashen duniya da ke sahun gaba wajen yawan adadin mutanen da ke garkame a gidajen yari, in da a shekarar 2014 kadai, ta kulle mutane fiye da dubu 600 a lokaci guda, kuma akasarinsu maza ne bakaken fata.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam na duniya sun sha kiraye-kirayen daukan mataki game da halin da mazauna gidan yari ke ciki a Brazil.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu