Isa ga babban shafi
Brazil

Brazil za ta tsuke bakin aljihu na shekaru 20

Majalisar Dattawan Brazil ta amince da wani shirin tsuke bakin aljihun gwamnati wanda za a ci gaba da aiwatarwa har tsawon shekaru 20 masu zuwa.

Mambobin Majalisar Dattawan kasar Brazil
Mambobin Majalisar Dattawan kasar Brazil 路透社
Talla

‘Yan Majalisar Dattawa 53 ne suka amince da wannan shirin, yayin da 16 suka ki amincewa da shi, abin da ke bai wa shugaban kasar Michel Temer damar aiwatar da shirin da wasu ke kallo a matsayin wanda ke dauke da sauye-sauye masu tarin yawa.

A karkashin wannan shirin, shugaba Temer ne ke da wuka da nama kan bangarorin da za a zaftare wa kudade, da suka hada sha’anin kiwon lafiya da ilimi da noma da dai sauransu.

To sai dai shugaban kasar ya ce, matakin zai taimaka sosai domin samar da ayyukan yi ga dimbin jama’a da ke zaman kashe wando a halin yanzu.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka shirya, ta tabbatar cewa kashi 60 cikin 100 na ‘yan kasar ne ke adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwmanatin.
 

A cikin makon jiya dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da tsarin, kuma a dai dai lokacin da majalisar ke zama kan wannan batu, yayin da aka jibge dimbin jami’an tsaro domin bayar da kariya ga gine-ginen gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.