Isa ga babban shafi
Amurka

Trump da Hillary za su gudanar da Muhawara Karshe

A yau Laraba ne dan takaran Shugabancin kasar Amurka Donald Trump da Hillary Clinton ta Democrats za su sake karawa a muhawara tsakanin su karo na uku, kuma na karshe kafin babban zaben kasar a watan Gobe.

Trump da Clinton a Muhawara su ta farko da ya dau hankali
Trump da Clinton a Muhawara su ta farko da ya dau hankali REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Za a tafka Muhawarar yau a jami’ar Nevada, Las Vegas, inda ake saran su kwashe awa daya da rabi suna fafatawa.

Wani gogaggen dan jarida Fox News da ke Amurka Chris Wallace, mai shekaru 69, ne zai shugabanci muhawaran na ‘yan takara biyu.

Akalla mutane miliyan 84 aka kiyasta sun kalle Muharawan farko da aka gudanar ranar 26 ga watan Satumban da ya gabata.

Donald Trump dai na ci gaba da bayyana furgaban zargin magudi a zaben shugabanci da ke tafi kasa da kwananki 20 masu zuwa a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.