Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta yi watsi da kalaman Trump kan NATO

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya bayyana cewa, kasar za ta ci gaba da aikin samar da tsaro na bai-daya da kasashen NATO kuma ya fadi haka don kwantar da hankulan kasashen Turai da suka nuna damuwa kan kalaman da Donald Trump ya yi a cikin watan Yulin da ya wuce. 

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry REUTERS/Jorge Silva
Talla

Kalaman dan takarar shugabncin Amurka karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump sun razana kasashen gabashin Turai, in da ya diga ayar tambaya kan yadda Washington ke mutunta doka ta biyar da ta kasance mafi muhimmanci ga kungiyar tsaro ta NATO, wadda ta bayyana cewa, kaddamar da hari kan kasa mambar kungiyar, tamkar kai hari ne kan ilahirin kasashen da ke kunshe a cikin NATO.

To sai dai Kerry ya ce, Amurka ba za ta taba mancewa da wannan doka wadda aka cimma matsaya a kanta a Arewacin Atlantic ba, musamma idan aka yi la’akari cewa, an fara aiki da ita ne gadan–gadan a lokacin da aka kai wa Amurka harin ranar 11 ga watan Satumba.

Mr. Kerry wanda ke magana a gaban kwararru a birnin Brussels na Belgim ya kara da cewa, Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mutunta wannan doka da zaran wata kasa, mamban NATO ta fuskanci hare-hare.

Kerry ya jaddada cewa, babu wani abu da Rasha za ta ji tsoransa daga NATO duk da sabanin da ke tsakaninta da kasashen Yamma kan mamaye yankin Crimea na Ukraine da ta yi da kuma yakin Syria.

A cikin watan Yulin da ya gabata ne, Donald Trump ya bayyana cewa, idan Rasha ta kai hari kan kasashen yankin Baltics, to lallai sai Washington ta fara nazari kan taimakakon tsaron da suka bai wa Amurka kafin ta kai musu dauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.